Akalla mutum 177 ne suka mutu a hadarin jirgin sama a kasar Koriya Ta Kudu

 Hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu ta ce aƙalla mutum 177 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman ƙasar bayan da wani jirgin saman fasinja ya kauce daga titinsa yayin da yake sauka a filin jirgin sama a Koriya ta Kudu.

Jirgin kirar Boeing 7-3-7 ya sauka kenan, bayan dawowa gida daga Bangkok na kasar Thailand, dauke da fasinjoji 175 da ma'aikatansa shida.


Saukar ta sa ke da wuya ne ya kwace ya saki titinsa ya kutsa ta cikin wani gini, kana ya kama da wuta.


Shaidu sun ce sun ji karar fashewar wani abu mai karfi bayan faruwar lamarin.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org