Amnesty Ta Zargi Shugaba Tinubu Da Jefa Yan Najeriya Cikin Kuncin Rayuwa
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya, Amnesty International, ta soki gwamnatin Najeriya karkashin shugabancin Bola Tinubu kan mutuwar mutane 65 a mako guda yayin turereniyar karbar shinkafa kyauta. Kungiyar ta danganta wannan matsalar da yunwa mai tsanani dake addabar Yan Najeriya. Wanda yayi silar mutuwar mutane da dama.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Asabar, Amnesty International ta nuna damuwa kan aukuwar wannan lamari a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, Abuja, da Okija a jihar Anambra cikin mako guda. Kungiyar ta ce, "A wannan makon, mutane 65 sun mutu a fadin Najeriya yayin turereniyar karbar shinkafa: a Ibadan yara 35 sun mutu, a Okija mutane 20 sun mutu, a Abuja mutane 10 sun mutu. Miliyoyin mutane na fuskantar yunwa da rashin abinci mai gina jiki, da talauci mai tsanani.
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ya kamata ta mayar da hankali kan magance yunwa, rashin aikin yi, da kuma faduwar darajar rayuwa cikin gaggawa."
A Ibadan, rahotanni sun nuna cewa yara 35 sun mutu a makarantar Islamiyya da ke Bashorun yayin wani taron Kirsimeti na yara. A Abuja, turereniyar da ta faru a cocin Holy Trinity Catholic Church a Maitama ta yi sanadiyar mutuwar mutane 10, ciki har da yara hudu, yayin rabon tallafi ga marasa galihu. Haka kuma, a Okija, an tabbatar da mutuwar mutane akalla 20 yayin turereniyar karbar shinkafa.
Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan gaggawa wajen magance matsalolin yunwa, rashin aikin yi.
Karaduwa post