An ba da Belin Tsohon Gwamnanan Kogi Yahaya BellCika Wasu Sharuɗɗan.

 An saki Yahaya Bello bayan cika sharuɗɗan belin. An sake shi da yammacin jiya Juma’a.”

An saki tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello daga gidan yarin Kuje bayan ya cika sharuɗɗan belin da babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama, Abuja ta gindaya.

Mai magana da yawun Hukumar gidan yari na ƙasa reshen babban birnin tarayya Abuja, Adamu Duza ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yammacin ranar Juma’a.

An saki Yahaya Bello bayan cika sharuɗɗan belin. An sake shi da yammacin jiyaJuma’a.”

“Kwanturola na hukumar gidan yarin na Abuja, Ajibogun Olatubosun, yana sane da umarnin don tabbatar da sakin sa kuma an cika dukkan sharuɗɗan.”

Mai shari’a MaryAnne Anenih ce ta bayar da belin Yahaya Bello a ranar Alhamis a kan kuɗi N500m.


Sharuɗɗan sun haɗa da gabatar da mutum uku, kowanne wanda ya mallaki kadarori a wasu wurare masu daraja a Abuja, kamar unguwannin Maitama, Guzape ko Asokoro.


Trust Radio

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org