Ƴan Bindiga sun sake dasa bam wanda ya yi sanadiyar kashe fasinjoji a kan hanyar Zamfara
Ƴan bindiga a yau Laraba sun sake dasa wani sabon jerin bama-bamai a yankin Mai Lamba da ke kan hanyar Dansadau zuwa Gusau a karkashin karamar hukumar Maru, jihar Zamfara, inda su ka kashe fasinjoji.
Hotunan da Channels Television ta samu sun nuna gawarwakin wadanda suka mutu suna kwance a gefen hanya yayin da matafiya suka tsaya suna kallon abin da ya faru cikin firgici da bakin ciki.
Mazauna yankin Dansadau sun shaida wa Channels Television cewa, 'yan ta'addan da ake zargin su ne suka dasa bama-baman a kan hanyar da ke hada Dansadau da sauran sassan jihar.
Wani mazaunin yankin mai suna Abdullahi Dansadau ya ce wata mota kirar Volkswagen Golf 3 ta taka bam din da aka dasa, wanda ya tarwatse kuma ya kashe mutane shida tare da jikkata wasu takwas.
"A safiyar yau ce, wata mota kirar Golf 3 ta taka bam din kuma ya tarwatse, yanzu haka muna da gawarwakin mutane shida nan, sannan wasu takwas sun samu raunuka, motar ta kone kurmus," in ji shi.
Sanarwa da Mataimakin Manjo, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, wanda shi ne Kodinetan Tsakiyar Hadin Kai na Kafafen Watsa Labarai, Operation Fansar Yamma, ya aikewa Channels Television, ta tabbatar da faruwar lamarin.Ƴan Bindiga sun sake dasa bam wanda ya yi sanadiyar kashe fasinjoji a kan hanyar Zamfara
Ƴan bindiga a yau Laraba sun sake dasa wani sabon jerin bama-bamai a yankin Mai Lamba da ke kan hanyar Dansadau zuwa Gusau a karkashin karamar hukumar Maru, jihar Zamfara, inda su ka kashe fasinjoji.
Hotunan da Channels Television ta samu sun nuna gawarwakin wadanda suka mutu suna kwance a gefen hanya yayin da matafiya suka tsaya suna kallon abin da ya faru cikin firgici da bakin ciki.
Mazauna yankin Dansadau sun shaida wa Channels Television cewa, 'yan ta'addan da ake zargin su ne suka dasa bama-baman a kan hanyar da ke hada Dansadau da sauran sassan jihar.
Wani mazaunin yankin mai suna Abdullahi Dansadau ya ce wata mota kirar Volkswagen Golf 3 ta taka bam din da aka dasa, wanda ya tarwatse kuma ya kashe mutane shida tare da jikkata wasu takwas.
"A safiyar yau ce, wata mota kirar Golf 3 ta taka bam din kuma ya tarwatse, yanzu haka muna da gawarwakin mutane shida nan, sannan wasu takwas sun samu raunuka, motar ta kone kurmus," in ji shi.
Sanarwa da Mataimakin Manjo, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, wanda shi ne Kodinetan Tsakiyar Hadin Kai na Kafafen Watsa Labarai, Operation Fansar Yamma, ya aikewa Channels Television, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Zamani Media Crew