Ƴan Nijeriya za su ga bunƙasar arziki da saukar farashin kayayyaki a 2025 - Bagudu

 Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren , Sanata Abubakar Bagudu, ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa tattalin arzikin ƙasar zai inganta a shekara mai zuwa duk da cewa gwamnati tana hasashen raguwar hauhawar farashi.

Bagudu ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa tare da wasu Ministoci bayan taro da Shugaba Bola Tinubu a Legas a ranar Lahadi.


Da yake magana kan sabbin manufofin gwamnati, Bagudu ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu wuya, kuma ƙasar ta sha gwagwarmaya mafi muni da za a iya tsammani.


"Don haka, abin da muke sa ran gani a shekarar 2025 shi ne tattalin arziki mafi kyau, raguwar hauhawar farashi, ƙarin damar samun aiki, ƙarin tallafi ga kasuwanci, da haɓaka gine-ginen more rayuwa.


"Muna kuma sa ran ƙarin kuɗaɗe don harkokin tsaro, da kuma waɗannan muhimman fannoni kamar bunƙasa  ilimi, kiwon lafiya. Mun tabbata za mu ga ci gaba a wannan ɓangaren, kuma rayuwar mutane za ta inganta," in ji Bagudu.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org