An rantsar da sabon shugaban ƙasar Georgia amma shugaba mai barin-gado ta ce sam ba za ta sauka ba
An rantsar da sabon shugaban ƙasar Georgia, Mikheil Kavelashvili, a daidai lokacin da ake zanga-zanga a Tbilisi babban birnin ƙasar.
BBC ta rawaito cewa a wani jawabin nuna rashin amincewa da wadda ya gada - Salome Zourabichvili - ta yi, ta ƙi sauka daga muƙamin, to amma ta fice daga fadar shugaban ƙasar.
Majalisar dokokin ƙasar - wadda jam'iyyarsa ta fi rinjaye ce ta zaɓi mista Kavelashvili, a matsayin shugaban ƙasar, a kwanakin da suka gabata
Ms Zourabichvili ta ce zaɓen nasa ya saɓa wa ƙa'ida, kasancewar zaɓen majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar cikin watan Oktoba na cike da kura-kurai.
An gudanar da bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar, bayan shafe makonni ana zanga-zangar adawa da jam'iyyar Dream Party ta Georgian, wadda 'yan adawa ke ganin ta ƙara samun ƙarfin iko da kuma adawa da EU.