An Samu Tashin Gobara inda ta laƙume wani kamfanin casar shinkafa ƙurmus a yankin Ega-Idah, Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Idah a Jihar Kogi.
Gobara ta laƙume wani kamfanin shinkafa ƙurmus a yankin Ega-Idah, Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Idah a Jihar Kogi.
Gobara ta laƙume wani kamfanin casar shinkafa ƙurmus a yankin Ega-Idah, Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Idah a Jihar Kogi.
Ganau sun ce da misalin ƙarfe 3 da dare kafin wayewar garin Alhamis ne gobarar ta tashi, bayan an ji ƙarar fashewar wani abu a wurin.
Sun bayyana cewa kamfanin da ke samar da shinkafar ga ’yan kasuwa a yankin ƙananan hukumomin Ibaji da Idah mallakin wasu ’yan kasuwa ne.
Wani shida ya ce wani mai gadi a kamfanin ya ba da rahoton jin sautin ƙyasta ashana kafin kafin ƙarar fashewar da aka ji a harabar kamfanin.
“Jim kaɗan bayan nan sai aka ji ƙarar fashewa da tashin wuta da ta laƙume ɗaukacin kamfanin.
Daily trust Radio