An tsare ‘yan Nijeriya 10,000 bisa laifin shige da fice a 2024 – Shettima

 Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa akalla ‘yan Nijeriya 10,000 ne aka tsare bisa laifukan shige da fice a kasashen Afirka da kasashen Turai a bana.

Sai dai ya yaba da irin gudunmawar da baki ‘yan Nijeriya ke bayarwa ga tattalin arzikin duniya, inda ya ce Nijeriya ce ke kan gaba a duk wani nau’in kudaden da ‘yan kasashen waje ke aikawa da su a yammacin Afirka.

Baya ga kudaden da ake aikewa daga kasashen waje, ya ce ‘yan Nijeriya dake zama a kasashen waje sun zama jakadu nagari wadanda suka yi fice a fannin fasaha, likitanci, wasanni, fasahar kere-kere, da sauran ayyukan da suka shafi al’umma. 

Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin a yayin taron shekara-shekara na ‘yan ci-rani karo na 10 na kasa mai taken, “Beyond Borders: Celebrating Migrant’ Legacy, Protecting their Rights,” a dakin taro na Banquet na fadar shugaban kasa, a birnin Tarayya Abuja.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org