An Yi Gangamin Taron Maulid kan Iyayen Annabi Muhammad S.A.W Jihar Katsina. Wanda wannan shi ne na farko a cikin jihar

 Daga Auwal Isah Musa.

Gamayyar 'Yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky da aka fi sani da Shi'a, sun gudanar da taron tunawa da Iyayen Manzon Tsira, Annabi Muhammadu (S)

Taron wanda ya gudana a A ranar Laraba 25 ga Disamban nan na 2024, a farfajiyar Markazinsu ta Katsina, ya samu halartar dandazon al'umma.

Sun bayyana taron a matsayin na karon farko da suka fara gudanawar a garin, wanda suka yi  suka yi masa laƙabi da ‘Ranar Iyaye Ta Duniya’ wato ranar da da tafi dacewa da ranar Mauludin Mahaifan Annabi Muhammad (S). 

Dan'uwan shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wato kanensa Shaikh Badamasi Yaqoub ne ya zama babban bako mai jawabi a taron, a yayin da Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ya zama mai jawabi na biyu.


Shaikh Badamasi Yaqoub a cikin Jawabinsa, ya bayyana cewar "Tun daga Annabi Adamu (A.S) har zuwa kan Mahaifin Annabi(S) Abdullahi, babu mushiriki ko daya a Nasabar Annabi (S), kamar yadda ayar ƙur’ani ta nuna yadda hasken Manzon Allah (S) ya riƙa ciratuwa zuwa tsatso daban-daban har ya iso kan Sayyid Abdullahi." -ya tabbatar


Shi kuwa a nasa jawabin, Shaikh Yakubu Yahya ya karanto Nasabar Annabi (S) da kuma Hadisai da suka tabbatar da Imanin mahaifan Annabi(S) wato Abdullahi da Amina.

Malamin ya kuma fadakar da 'ya'yaye wajibcin biyayya ga iyayensu, su ma Iyaye aka fadakar da su nauyin 'ya'yayensu a kawukansu.


A wajen taron, an karrama mahaifan Shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky. Hakazalika, an kuma karrama da kuma mahaifan shehin Malami, Shaikh Yakubu Yahya Katsina.


Sannan kuma har wayau, an yanka Alkaki da raba kyautuka don murna da ranar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org