Ƴansanda sun cafke ƴan daban 'Shila' 3 bisa laifin fashi da makami a Adamawa
Rundunar ƴansanda a jihar Adamawa ta cafke wasu ƴan kungiyar dabanci da ake kira da yan Shila a garin Yola bisa zarginsu da yin fashi.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Adamawa, Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Asabar a Yola.
Nguroje ya ce ƴansanda sun samu sahihan bayanai cewa biyar daga cikin yaran na yin fashi a kan titin Bishop da ke unguwar Jimeta a Yola da sanyin safiya.
Da isar su wurin, sai yaran su ka far wa jami’an ‘yan sanda da adduna da kuma wukake a kokarin da su na tirjiya daga kama su.
A kokarin dakile harin, a cewar sa, sai ƴansanda su ka yi an yi amfani da karfi, su ka kama mutane uku da ake zargi, yayin da wasu biyu suka tsere.” Inji shi.
A cewarsa, abubuwan da aka samu a hannunsu sun hada da adduna, wukake, katin ATM, wayoyi, da babur mai kafa uku.
Ya ce wadanda ake zargin yanzu haka suna taimakawa a binciken da ake yi.