Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kuɗi naira miliyan 500.

 A zaman da kotun ta yi a yau Juma'a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Emeka Nwite, kotun ta buƙaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa domin samun belin.

Alƙalin ya ce dole ne mutanen da za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja, babban birnin ƙasar.

Haka kuma kotun ta ce dole ne masu tsaya masan su gabatar wakotun takardun kadarorin nasu domin tantancewa.

A baya-bayan nan ne dai hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi a gaban kotu bisa zarge-zarge 19 da suka ƙunshi almundahanar kuɗaɗe da yawansu ya kai naira biliyan 80.

Lamarin da ya sa kotun ta tura shi gidan gyaran hali, a yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar.

Sai dai Yahaya Bello ya musanta aikata ba daidai ba.

Mai shari'a Nwite ya ce dole ne tsohon gwamnan ya ajiye fasfo ɗinsa na tafiye-tafiye.

Haka kuma ya bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da zai cika sharuɗan beli.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai babbar kotun Abuja ta tura tsohon gwamnan gidan yarin Kuje bayan fatali da buƙatar belinsa kan zarge-zargen karkartar da sama da naira biliyan 100 a lokacin da yake gwamnan jihar da ke tsakiyar Najeriya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org