BABBAR MAGANA: Sowere ya Ƙalubalanci EFCC Kan Jinkirin Kama Buhari, Aisha da Malami

 Dan gwagwarmaya, kuma shugaban dake jagorantar #RevolutionNow, Omoyele Sowore ya Ƙalubalanci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC kan Jinkirin da suka yi wajen kama tsohon shubaban kasa, Muhammadu Buhari da mai dakinsa, Aisha Muhammadu Buhari da kuma Ministan shari'a na zamanin su wato Abubakar Malami, SAN, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban gazawa.

Omoyele Sowore ya bayyana hakan ne a dukkan shafukansa na yanar gizo, tun daga Facebook har sauran shafukan baki daya, inda yake Ƙalubalantar hukumar ta EFCC da zargin ba da gaske take aikin ta ba matukar bata kama wadannan mutane ba.

Bugu da kari, Sowere ya bayyana mutanen a matsayin wanda suka azurta kawunansu da dukiyar al'ummar Kasar ta hanyar sata, inda ya zargi, Sabiu Tunde da yin gagarumar satar da ba'a taba zato ba.

@Sahara Reportes Hausa 



Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org