Bafarawa Ya Ce "Za mu ceto arewa da ɗora matasan yankin kan shugabanci"

 Tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Ɗalhatu Attahiru Bafarawa ya ce sun ƙaddamar da wata gwagwarmaya ta ceto arewacin Najeriya da kuma zaburar da matasan yankin.

A wannan makon ne, wasu jiga-jigan ƴansiyasa daga arewacin Najeriya suka ƙaddamar da wata tafiya da suka kira da sunan Northern Star Empowerment Initiative ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ɗalhatu Attahiru Bafarawa kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto.

Sun ce manufar ƙungiyarsu ita ce haɗa kan al'ummar yankin da ɗora matasa kan shugabanci.

A hirarsa da BBC, Alhaji Bafarawa ya ce sabon yunƙurinsu na da alaƙa da tsamo arewacin Najeriya daga matsalolin da yankin ke fama da su, kamar na taɓarɓarewar tsaro da rashin aikin yi da ƙaruwar fatara, baya ga ƙarancin abinci da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

BBC HAUSA 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org