Bayan Dangote, NNPC ma ya rage farashin litar man fetur
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya rage farashin litar Man Fetur zuwa N899 a kowace lita.
Ana sayar da man dai a baya kan N1,020.
A cewar Ƙungiyar Ma’aikatan Tashoshin Sayar da Man Fetur ta Najeriya (PETROAN), NNPCL ne ya sanya wannan sabon farashin.
Da ya ke nakalto wata takarda da Sashen Kasuwanci na NNPCL ya fitar, jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na ƙungiyar, Dakta Joseph Obele, ya bayyana cewa rage farashin ya danganta ne da tsarin farashi na yankuna, inda ya bayyana cewa, karkashin wannan tsarin, za a sayar da shi kan N970 a kowace lita a wasu sassan yankin Kudu maso Kudu.