Cristiano Ronaldo na sha’awar komawa addinin musulunci - Rahoto
"Na yi magana da shi (Ronaldo) game da hakan, kuma ya nuna sha'awa. Ya riga ya yi sujada a filin wasa bayan ya zura kwallo a raga, kuma a kodayaushe yana kwadaitar da ‘yan wasan da su rika yin addu’a da bin tsarin addinin Musulunci,” in ji tsohon mai tsaron ragar Al-Nassr Waleed Abdullah.
"Lokacin da akeyin kiran salla a lokacin horo, Ronaldo ya bukaci kocin ya dakata har sai an kammala," Abdullah ya fadi.
"Lokacin da Cristiano Ronaldo ya yi sujjada a filin wasa bayan ya zura kwallo a raga, dukkan 'yan wasan sun yi ihun "Allahu Akbar" baki daya."
#DailyTrueHausa