Daga Yanzu 'Yan Najeriya Zasu Iya Kai Ziyarar Yawon Buɗe Ido Kasar Afrika Ta Kudu Batare Da Fasfo Ba.

 Jaridar Rana24 ta ruwaito Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa a yanzu 'yan yawon bude ido na Najeriya za su iya neman biza ba tare da gabatar da fasfo ba. 

Ramaphosa ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 3 ga watan Disamba a yayin bude taro karo na 11 na kungiyar hadin kan kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu (BNC) a birnin Cape Town, wanda ya samu halartar shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa, Afirka ta Kudu ta sauƙaƙa hanyoyin bizarta don saukaka tafiye-tafiye ga ‘yan kasuwa da masu yawon buɗe ido a Najeriya, inda ta bullo da wasu matakai kamar biza na shekaru biyar.

“Kokarin da muka yi na samar da yanayi mai kyau ya hada da saukaka tsarin biza ga ‘yan kasuwan Najeriya da ke tafiya Afirka ta Kudu. An bai wa ’yan kasuwar da suka cancanta ‘yan kasuwan Najeriya takardar izinin shiga da yawa na shekaru biyar,” inji shi.

Shugaban ya kuma jaddada aniyar Afirka ta Kudu na kawar da shingayen kara zuba jari da magance kalubalen da kamfanoni ke fuskanta a kasashen biyu.

“Yayin da muka cika shekaru 30 na huldar diflomasiyya, mun ga kyakkyawar makoma ga dangantakarmu. Dangantakar abokantakarmu ta samar da ginshiki mai inganci na hadin gwiwa a fannin tattalin arziki," in ji Ramaphosa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org