Dalilan da suka sa Tinubu da majalisa suka dakatar da ƙudirorin dokar haraji
A ranar Laraba ne Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da jingine aiki kan ƙudirin dokokin haraji na ƙasar, wanda Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gabatar mata.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin - wanda ya jagoranci zaman - shi ne ya sanar da hakan yayin da suke muhawara zauren majalisar.
Barau ya kuma sanar da kafa wani kwamati da zai yi aikin dubawa da kuma gyara saɗarorin dokar da ke jawo taƙaddama, musamman daga yankin arewacin ƙasar.
A makon da ya gabata ne ƙudirorin huɗu suka tsallake karatu na biyu a majalisar, daga nan kuma Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya miƙa wa kwamatin kuɗi domin ci gaba da aiki a kansu kafin karatu na uku kamar yadda dokar majalisa ta tanada.
"Muna farin ciki shugaban ƙasa ya ji koke-koken mutane, amma da ma mu ba mu niyyar amincewa da wannan ƙudiri ba," in ji Sanata Abdul Ningi cikin wata hira da BBC jim kaɗan bayan ɗaukar matakin.
Wasu daga cikin sanatocin kwamatin sun haɗa da Titus Zam (jihar Binuwai), da Orjir Uzor Kalu (jihar Abia), da Sani Musa (jihar Neja), da Abdullahi Yahaha (jihar Kebbi).
Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan Shugaba Tinubu ya umarci ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta yi aiki tare da majalisar dokokin domin samun masalaha kan wasu ɓangarori na dokar da ake taƙaddama a kai.
Tattaunawa kan ƙudurin ta janyo zazzafar muhawara a faɗin Najeriya, yayin da wasu ɓangarorin ƙasar suka yi zargin cewa an cusa wasu abubuwa da za su cutar da wasu yankunan ƙasar.
Me ya sa Tinubu ya ce a dakata?
A yammacin Talata ne Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya fitar da sanarwar da ta bayyana cewa shugaban ƙasa ya umarci ma'aikatar shari'a ta haɗa kai da majalisar domin duba ɓangarorin dokar.
Sanarwar ta bayyana cewa Tinubu na maraba da muhawara "mai amfani", tana mai zayyana dalilan da suka sa aka bayar da umarnin, kuma ciki har da "labaran ƙarya da ake yaɗawa" kan dokar.
"Ya kamata a lura cewa akwai ƙarairayi da labaran ɓata suna da ake yaɗawa game da ƙudirorin dokar da ma sauran manufofin gwamnatin Tinubu," a cewar ministan.
"Yana da kyau mu bayyana cewa babu wata maƙarƙashiya da gwamnati ta shirya da zai sa a dinga tunanin dalilin da ya sa take yin gaggawa kenan kan fara aiki da dokar.
"Saboda haka ne Shugaba Tinubu ya bai wa Ma'aikatar Shari'a ta Ƙasa da jami'an da suka yi aiki kan ƙudirin domin su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da majalisar dokoki domin tabbatar da cewa an gyara duk wata damuwa da ake da ita kafin amincewa da dokar."
Ministan ya jaddada batun cewa dokokin "ba za su cuci wata jiha ko yanki na ƙasar ba, haka ma ba za su kai ga rushewa ko rage wa wata ma'aikatar gwamnatin tarayya ƙarfi ba".
Ba lokaci ne da ya dace ba'
A makon da ya gabata ne ƙungiyar 'yanmajalisa daga arewacin Najeriya ta ce ta yanke shawarar yin watsi da ƙudiroriin da zarar an fara muhawara a kansu a zauren majalisar.
Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Mazaɓar Bauchi ta Tsakiya shaida wa BBC cewa ba maganar dakatar da dokar kawai suke yi ba yanzu.
"Wannan ƙudiri bai kamata a kawo shi yanzu ba...ba wai maganar dakatar da dokar ba ne, muna ƙalubalantar lokacin da aka kawo dokar harajin," kamar yadda sanatan na jam'iyyar PDP ya bayyana.
"Abu ne da ya kamata a ce sai an tattauna, sai an ga dalilai. Babu dalilin da za a kawo maganar haraji yayin da aka cire tallafin mai, [farashin] dala ya ninka kusan sau biyar, ta ina ɗan'adam zai iya yin rayuwa a haka?"
Shi ma Sanata Ali Ndume ya bayyana abubuwa uku da ya ce su ne suka sa yake adawa da ƙudirorin, waɗanda ya ce har yanzu ba su sauya ba.
"Na ɗaya, ba a tuntuɓi gwamnoni da shugabanninmu ba. Na biyu, ba wannan lokacin ya kamata a yi maganar haraji ba. Na uku, maganar yadda za a dinga rarraba harajin VAT ya saɓa wa doka," in ji sanatan na jam'iyyar APC.
Waɗanne ne ƙudirorin harajin?
A farkon watan Oktoban wannan shekarar ne Bola Tinubu ya aike da wasu ƙudurorin huɗu gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewarta.
Manufarsu ita ce yin kwaskwarima kan yadda ake karɓa da raba kuɗaɗen haraji a Najeriya ta hanyar ƙirƙira da kuma maye gurbin wasu hukumomi.