Dalilin da ya sa gwamnatin taraiya ba ta fara baiwa ƙananan hukumomi kuɗin su kai-tsaye ba -- Kungiyar Ciyamomi
Gwamnatin Tarayya ba ta fara biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye zuwa asusun su ba duk da hukuncin da Kotun Koli ta yanke watanni hudu da suka gabata.
A watan Yuli, Kotun Koli ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta rika biyan kudaden wata-wata kai tsaye ga asusun kananan hukumomi 774 da ke kasar.
Sai dai har yanzu, watanni hudu bayan hukuncin, kudaden na ci gaba da shiga cikin asusun hadaka na jihohi da kananan hukumomi ta hanyar Hukumar Raba Kudaden Tarayya (FAAC).
A wata zantawa da jaridar The Punch, mai magana da yawun Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), Obiora Orji, ya tabbatar da cewa ba a fara biyan kudaden kai tsaye ga ƙananan hukumomi ba.
“Wannan shi ne abin da kowa ke jira. Ba zai iya boyuwa ba, domin da zarar an fara biyan kudin, kowa zai sani,” in ji Orji.
A nashi tsokacin, Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Ƙasa , (NULGE), Akeem Ambali, ya bayyana cewa jinkirin yana da nasaba da rashin amincewar Shugaba Bola Tinubu wajen aiwatar da cikakken ‘yancin cin gashin kai na kudi ga kananan hukumomi.
Daily Nigeria Hausa