Dokokin cin zaɓen shugaban ƙasar Ghana.

 Miliyoyin 'yan ƙasar Ghana ne ke zaɓar sabon shugaban ƙasa da 'yan majalisa a yau Asabar wanda zai jagorancin ƙasar nan da shekara huɗu masu zuwa.

Zaɓen na zuwa yayin da Shugaba Nana Akufo Addo ke kammala wa'adin mulkinsa na biyu.

A ƙarƙashin dokokin kundin tsarin mulkin ƙasar, ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da na 'yan majalisar dokoki

'Yan takara 12 ne ke fafatawa a zaɓen, sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin manyan jam'iyyu biyu, wato NPP mai mulki da kuma NDC mai hamayya.

Akwai kuma 'yan takara biyu na indifenda, waɗanda ake ganin za su yi tasiri wajen kwashe ƙuri'u masu yawa.

Lamarin dai ya sa masu sharhi a ƙasar na hasashen zuwa zagaye na biyu a zaɓen na bana.

Kundin tsarin mulkin ƙasar dai ya yi tanadin zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar, idan babu ɗan takarar da ya samu rinjaye a zagayen farko.

Kan haka ne muka duba abin da ɗan takara ke buƙatar samu kafin hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Abin da ɗan takara ke buƙatar samu

Hukumar zaɓen ƙasar ce dai kaɗai ke da alhakin ayyana sakamakon zaben bayan tattara shi daga mazaɓun ƙasar 4,975.

Irbat Ibrahim, wani mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullum a ƙasar, ya kuma shaida wa BBC cewa kundin tsarin mulkin Ghana ya yi tanadin cewa dole ne ɗan takara ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa kafin ayayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

''Matsawar ɗan takarar bai samu wannan adadi ba, koda kuwa ya samu kashi 49.99, to bai ci zaɓen shugaban ƙasar Ghana ba'', in ji masanin.

Kundin dokokin zaɓen ƙasar da aka yi wa gyara a 1996, ya tanadi cewa idan babu ɗan takarar da ya samu fiye da kashi 50 na ƙuri'un, dole ne a shirya zaɓen zagaye na biyu a cikin kwana 21 bayan zaɓen farko.

Yaya ake zaɓen zagaye na biyu?

Irbat Ibrahim ya ce idan za a je zagaye na biyu a zaɓen ƙasar manyan jam'iyyu biyun da ke kan gaba ne za su fafata a zaɓen.

''A zagaye na biyun duka ƙananan jam'iyyun ba za su shiga zaɓen ba, a maimakon haka za su goyi bayan ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun'', kamar yadda kundin dokar zaɓen ya nuna.

Sannan kuma ana gudanar da shi ne mako uku bayan gudanar da zaɓen na farko.

A cikin shekara 30 da suka gabata, zaɓukan ƙasar na gudana ne cikin lumana duk da cewa suna zafi matuƙa.

Hakan ya sa ake wa Ghana kallon zakarar gwajin-dafi saboda duk da fama da juyin mulki da ta sha a baya, yanzu dimokuraɗiyyarta na tafiya da kyau.

Sannan duk da cewa a wasu lokutan a kan samu masu ƙalubalantar sakamakon zaɓen, yawancin waɗanda suka sha kaye suna amincewa da sakamakon zaɓen.

Muna na sa ran samun sakamakon zaɓen na bana a cikin kwana uku daga ranar 7 ga Disamba da aka kaɗa ƙuri'a.

@BBC HAUSA 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org