Duk samarin da na taɓa yi sai da su ka yaudare ni - Tiwa Savage
Shahararriyar mawakiyar 'Afro-pop' ɗin Najeriya, Tiwa Savage, ta bayyana ra'ayinta kan cin amana a cikin alaƙa, tana nuna cewa wannan ba ya zama dalilin rabuwa gare ta.
Wasu dai na ganin cewa mawakiyar ba ta da sa'a a soyayya. Ta bayyana wannan ra'ayi nata a wani shirin faɗar ra'ayi na 'The Receipts' da Tolly T da Audrey ke gabatarwa.
Mawakiyar ta bayyana cewa ƙarya ita ce mafi zafi a gare ta fiye da cin amana kanta. Ta ce matsaloli masu tsanani irin su shaye-shaye, wulakanci ta fannin tunani, da barin mutum haka kawai, su ne abubuwan da ba za ta lamunta ba.
"Ban taɓa barin namiji saboda ya ci amanata ba. Na taɓa rabuwa saboda dalilai da dama irin su shaye-shaye, wulakancin , da barina haka kawai,” in ji Tiwa Savage. Tun bayan da aurenta da TeeBillz ya mutu a shekarar 2016, Tiwa Savage ta yi alaƙa da manyan mutane daban-daban.
Rayuwarta ta sirri ta sha fuskantar sukar jama'a, ciki har da batun faifan bidiyon ta mai rikitarwa da ya bayyana. Amma duk da abubuwan da ta sha fuskanta a baya, Tiwa Savage ba ta daina fatan samun soyayya ba. Sai dai, ta bayyana sarai abubuwan da ba za ta amince da su a cikin alaƙa ba.