Gidan talabijin mai zaman kansa na farko a Nijeriya ya rufe sakamakon tsadar wutar lantarki

 Mahukunta a kamfanin DESMIMS BROADCAST NIG. LTD, wanda ya ke da gidan talabijin DITV Kaduna da gidan rediyon Alheri sun sanar da dakatar da ayyukansu har sai baba-ta-gani.

Tashar Talabijin din ita ce tasha mai zaman kanta ta farko da ta fara aiki a ranar 2 ga watan Yuni, 1994.

A wata sanarwa da mukaddashin babban manajan gidan talabijin din, Idris Mustapha ya fitar a ranar Juma’a, ta ce an dauki matakin ne saboda tsadar wutar lantarki.

Sai dai ya ce matakin bai shafi gidan rediyon Alheri da ke Zariya ba.

Mustapha ya yi nuni da cewa, tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar nan ya sa samar da kudaden shiga ya zama kalubale ga ‘yan kasuwa da dama.

Yayin da ya ke nuna rashin jin dadi da takura da rufewar zai haifar da miliyoyin masu saurare da kallon tashar, Mustapha ya ce gidan rediyon zai koma bakin aiki da zarar yanayin kudin shiga ya inganta.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org