Google, Microsoft, TikTok, sun biya haraji na Naira tiriliyan 2.55 a Najeriya a watannin 6 da suka gabata – NITDA

 Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) ta bayyana cewa kamfanonin fasahar zamani na ƙasashen waje da ke aiki a Najeriya, ciki har da Google, Microsoft, da TikTok, sun biya jimillar haraji na Naira tiriliyan 2.55 a rabin farkon wannan shekarar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta hannun Daraktar Hulɗa da Jama’a da Kafofin Watsa Labarai, Hajiya Hadiza Umar, inda ta zayyana bayanai daga Hukumar Kula da Haraji ta Ƙasa (FIRS) da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS).

NITDA ta jinjina wa Google, Microsoft, X, da TikTok musamman saboda biyayyar su ga Dokar Aikin Dandamalin Sadarwa na Zamani da Masu Tsaka-tsakin Intanet.

Dokar, wacce Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), Hukumar Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC), da NITDA suka fitar tare, ta ƙunshi ƙa’idoji masu bayani kan inganta amincin amfani da intanet da kuma kula da abun da zai iya zama mai lahani.

Dokoki suna samar da kyakkyawan sakamako

Yayin da NITDA ta haskaka tasirin wannan tsarin doka, ta nuna cewa hakan ya ƙara haɓaka kuɗaɗen shiga na gwamnati ta hanyar biyan haraji daga kamfanonin fasahar zamani.

“Bayanai daga Hukumar Kula da Haraji ta Ƙasa (FIRS) da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna cewa kamfanonin fasahar zamani na ƙasashen waje, ciki har da dandamalin sadarwa na zamani da masu tsaka-tsakin intanet (kamar kafofin sada zumunta) da ke aiki a Najeriya, sun bayar da sama da Naira tiriliyan 2.55 (kimanin dala biliyan 1.5) a matsayin haraji a rabin farkon shekarar 2024.

“Wannan gagarumin ci gaba a kuɗaɗen shiga na nuna muhimmancin tsarin dokoki masu ƙarfi wajen inganta biyayya da haɓaka ci gaban tattalin arziƙin zamani,” in ji NITDA.

#Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org