Gwamnan Katsina Ya Amince da Fara Rage Kashi 7% ga Albashin Ma'aikatan jiha A Matsayin Fansho

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya amince da fara rage kaso bakwai (7) a cikin ɗari (100) daga albashin ma’aikatan gwamnatin jiha, kananan hukumomi, da hukumomin ilimi na kananan hukumomi. 

Wannan sabon tsarin dai zai fara aiki daga watan Disamba 2024, bisa tanadin Dokar Fansho ta jiha wadda aka sa ma hannu a shekarar 2022 watau, Katsina State Contributory Defined Benefits Pension Law, 2022 a turance

Dokar dai ta tanadi cire kaso 7% daga jimillar albashin kowane ma’aikaci a matsayin gudunmowar su ga tsarin fanshon, kamar yadda aka tanada a sassan 4(2) da 6 na dokar. 

Wannan mataki ya biyo bayan yarjejeniyar da gwamnatin jiha ta cimmawa tare da ƙungiyoyin ƙwadago na jihar kan sabon tsarin albashi mafi ƙanƙanci na ₦70,000 da Gwamnan ya amince da shi a watan da ya gabata

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org