Gwamnati Tarayya ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa
A jiya juma’a ne Gwamnatin Tarayya ta fara jigilar fasinjoji a jiragen ƙasa kyauta a faɗin ƙasar domin sauƙaƙa tsadar sufurin fasinjoji a faɗin ƙasar a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
Jigilar fasinjojin za a riƙa yinta cikin lumana a wurare biyar da suka haɗa da: Abuja zuwa Kaduna da Lagos zuwa Ibadan da Warri zuwa Itakpe da Portharcourt/Aba
Muƙaddashin Manajan Daraktan Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC), Ben Iloanusi a lokacin da yake maraba da rukunin farko na fasinjojin da suka isa tashar jirgin ƙasa ta Kubwa da ke Abuja daga Rigasa, ya ce Hukumar ta nuna damuwa kan yadda za a kare lafiyar fasinjoji a ranar farko.
Da yake jawabi, ya kuma bayyana cewa “jigilar fasinjojin kyauta zai ɗauki fasinjoji 20,000 a kullum domin gwamnatin tarayya ta yi ƙiyasin yin jigilar kyauta ga fasinjoji 340,000 kafin wa’adin jigilar ya ƙare a makon farko na watan Janairu.”
Ya ƙara da cewa, jigilar fasinjojin za a riƙa yinta cikin lumana a wurare biyar da suka haɗa da: Abuja zuwa Kaduna da Lagos zuwa Ibadan da Warri zuwa Itakpe da Portharcourt/Aba da kuma Lagos Mass Transit.

#Trust Radio