Gwamnati tarayya ta ware Naira biliyan 1.83 don mayar da gidajen da EFCC ta ƙwace zuwa gidajen Fadar Shugaban Ƙasa

 Gwamnatin Tarayya ta gabatar da shirin kashe Naira biliyan 1.83 a kasafin kuɗin 2025 don mayar da wasu gidaje da Hukumar EFCC ta ƙwace zuwa gidajen Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.

A cewar tsarin kasafin kuɗin 2025 da aka gabatar, an ware Naira biliyan 1,830,783,061 don  gyaransu, da kuma farfaɗo da su domin su zama gidajen zama na Fadar Shugaban Ƙasa.

Haka zalika, an ware Naira miliyan 120.28 don gyaran gidajen jami'an tsaron Fadar Shugaban Ƙasa.

Binciken Nairametrics ya kuma gano cewa an ware Naira biliyan 5.49 don kula da fadar shugaban ƙasa na shekara-shekara, wanda ke nuna  kuɗi da aka tanada don tabbatar da nagartar wannan cibiyar ta ƙasa.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org