Gwamnatin Jihar Katsina Ta Shimfida Sharudda Kan Halartar Daliban SS3 Zuwa Jarrabawa

Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Katsina ta bayyana damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa wasu daliban SS3 sun daina halartar ajinsu bayan kammala jarrabawar cancanta.  

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar 5 ga Disamba, 2024, wacce Babbar Sakatariya, Ummulkhairi Ahmad Bawa, ta rattaba wa hannu, an bayyana cewa duk dalibi dole ne ya samu kashi 75% na halartar darussa kafin a ba shi damar yin rijista da jarrabawar waje irin su WAEC, NECO, NABTEB, da NBAIS.  

Har ila yau, ma’aikatar ta ce daliban da ba su cika wannan ka’ida ba ba za a dauke su a matsayin dalibai da gwamnati ta dauki nauyin su ba, ko da sun ci jarrabawar cancanta. An umarci shugabannin makarantu su tabbatar da cewa an yi aiki da wannan doka don dakile matsalar kauracewar dalibai daga aji.


Ma’aikatar ta yi kira da a dauki matakin nan da gaggawa domin tabbatar da ingantaccen bin doka da oda.

@Rana24




Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org