Gwamnatin Kano ta magantu kan girke jami'an tsaro a gidan Sarkin Kano

 Gwamnatin Jihar Kano, ta bakin Sakataren Gwamnatin, Dakta Baffa Bichi ta yi alla-wadai da ganin jami'an tsaro sun yi wa fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ƙawanya.


DAILY NIGERIAN HAUSA ta ruwaito cewa a yau safiyar Juma'a an tashi da ganin jami'an ƴansanda ɗauke da makamai tare da na SSS sun yi ƙawanya a Masarautar Kano, inda Sarki Muhammadu Sanusi ll ke zaune.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa jami'an tsaron sun hana shige da fice a gidan Sarkin.

Rahotanni sun baiyana cewa a yau din ake sa ran Sarki Sanusi zai raka sabon Wamban Kano, Munir Sanusi zuwa Bichi, inda zai yi hamkimci.

DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa can ma fadar harkokin na Bichi an zuba jami'an tsaro, mai yiwuwa da nufin hana zuwan sabon Wamban.

Sai dai kuma da ya ke sanyawa da gidan Freedom Radio, Bichi ya ce hakan wani yunkuri ne na haifar da rikici a Kano.

Sai dai ya ce gwamnatin Kano ba za ta biyewa duk wani yunkuri na tada hankalin al'umma ba.

A cewar sa, ko da gwamnatin ta tambayi jami'an tsaron akan dalilin da ya sa su ka mamaye fadar, sai su ka ce wai umarni ne da ga sama.

Ya yi alla-wadai da wannan ta'adda, inda ya zargi gwamnatin tarayya da hannu wajen wannan lamari.

Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org