Gwamnatin Nigeriya ta fara biyan sojojin ƙarin albashi da sauran hakkokin su - Matawalle
Gwamnatin Taraiya ta sanar da cewa ta fara biyan karon albashin sojoji, har da ma na watanni ukun baya daga lokacin da aka tabbatar da ƙarin.
Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da Henshaw Ogubike, kakakin ma'aikatar tsaron ta fitar.
Ya kara da cewa tuni sojojin kasar su ka fara jin alat a wayoyin su.
Daily Nigeria Hausa