Gwamnatin Taraiya ta ware Naira biliyan 27 da za a rabawa Buhari, Jonathan, Obasanjo da sauran su
Gwamnatin tarayya ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan 27 domin biyan tsofaffin shugabannin kasa, mataimakan su, shugabannin kasa na mulkin soji, shuwagabannin ma’aikata masu ci da wadanda su ka ritaya da kuma malaman jami’a da suka yi ritaya a kasafin kudin 2025, kamar yadda wani bincike da jaridar PUNCH ta gudanar a yau Asabar ya nuna.
Wadanda za su ci gajiyar wannan kason sun hada da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, da Muhammadu Buhari, da Umaru Musa Yar'adua tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Namadi Sambo, da Farfesa Yemi Osinbajo.
Sauran wadanda ake sa ran za su ci gajiyar kuɗaɗen sun hada da tsohon shugaban kasa na soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) da kuma Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), da kuma tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida da babban hafsan sojin kasa, Commodore Ebitu Ukiwe mai ritaya da sauran su.
A ranar Laraba ne dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025 sanya kai N49.70tn a gaban majalisun taraiya.