Hukumar Hisba ta jihar Kano ta sanya dokar tashi daga gidajen bukukuwa zuwa karfe 11 na dare.

 Hukumar ta bayyana hakanne ta cikin wata sanarwa da ta fitar ta bakin mataimakin babban kwamandan hukumar Shekh Mujahideen, inda yakara da cewa wajibine duk mamallaka gidajen bukukuwan su rika tashi kafin karfe goma shadaya nadare tare da tsayar da duk abinda akeyi a kimanin mintina goma sha biyar, dimin yin Sallah.

Yakuma kara dacewa kasancewar jihar kano garine na musulinci yasanya hukumar taga dacewar sake jaddada wadannan dokoki na kaucewa cakuduwar maza da mata dakuma yin amfani da kade-kade masu kara ana shiga hakkin makobta, inda ya tabbatar da cewar dokokin zasu fara aikine daga ranar 1 ga watan janairu 2025, me kamawa.


Menene ra'ayinku a Kan wadannan dokokin?

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org