Hukumar Zabe Ta Kasa INEC ta yi watsi da batun mutuwar shugabanta Mahmood Yakubu

Hukumar zaɓe a Najeriya INEC, ta yi watsi da rahotanni da ake yayatawa kan mutuwar shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, wanda ya samu sa hannun sakataren yaɗa labaran shugaban, Rotimi Oyekanmi, ya ce labarin kanzon kurege ne.

Sanarwar ta ce: "hankalin mu ya kai ga labaran karya da ake yaɗa wa a kafafen sadarwa da ke iƙirarin cewa shugaban hukumar zaɓen Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya mutu a wani asibiti a birnin Landan. Wannan ba gaskiya bane," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce mutane su yi watsi da labarin mutuwar shugaban na INEC, inda ta ce yana cikin koshin lafiya, kuma bai ma yi wata tafiya zuwa birnin Landan ba a cikin shekaru biyu da suka wuce.

An dai fara yayata batun mutuwar Farfesa Yakubu a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba a kan kafofin sada zumunta.

Sai dai INEC ta ce shugaban nata ya ma halarci wani zama da kwamitin majalisar wakilai kan ɓangaren zaɓe ranar Laraba, 11 ga Disamban 2024.

BBC HAUSA 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org