Idan an kawo mutum asibiti da harbin bindiga a kula da shi ko ba ɗansanda -- Ma'aikatar lafiya

 Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya ta bada umarnin cewa dukkan asibitoci  na gwamnati da masu zaman kansu a fadin ƙasa da su kula da waɗanda aka harba, ko da su na da takardar izinin ƴansanda ko babu.

Wannan umarni yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya da Jin Kai ta fitar a ranar Asabar ta hannun shafinta na X na hukuma.

Sanarwar, mai taken ‘Rashin Bin Dokar Kula da Masu Raunin Harbi ta 2017’, wacce Daraktar Bayanai, Patricia Deworitshe, ta sa hannu, ta bayyana cewa ma’aikatar ta karɓi korafe-korafe akan yadda asibitoci a fadin ƙasa ke ƙin karɓar masu raunin harbin bindiga, wanda hakan ke haifar da asarar rayuka.

Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa umarnin ya zo ne bisa jagorancin Ministan Tsare-tsaren Lafiya da Jin Kai, Farfesa Muhammad Pate.

A cewar sanarwar, waɗanda aka harba sukan shiga cikin gaggawa, wanda ke buƙatar kulawar lafiya cikin sauri domin ceto rayukansu.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org