Jam'iyyar APC Tasha Alawashin kwace mulkin Jihar adamawa daga hannu Jam'iyyar PDP a Zaben 2027.
Gabanin zaben 2027, jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihar Adamawa sun lashi takobin samar da wasu matakai da nufin kawar da jam’iyyar PDP karkashin Gwamna Ahmadu Fintiri daga jihar.
A bisa tabbatar da wannan manufa, kwamitin sulhu na jam’iyyar APC karkashin jagorancin Sanata Muhammed Mana, ya gana da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, a ranar Alhamis a Abuja.
Tawagar sulhu mai mutane takwas ta hada da fitattun ‘yan siyasa irin su Sanata Bello Tukur, Abubakar Girei, da Binta Masi, da kuma Hon. Yusuf Buba Yakubu, Dr. Bridget Zidon, da Barr. Isa Baba, wanda ke zama Sakatare.
Menene ra'ayinku?