Jam'iyyar PDP ta ce "Ba ma zawarcin Jonathan a takarar 2027"

 Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta ce babu ƙanshin gaskiya a rahotannin da ake yaɗawa cewa ta nemi tsohon shugaban ƙasar, Dokta Goodluck Ebele Jonathan da ya tsaya mata takarar kujerar shugabancin ƙasar a shekara ta 2027.

Jam'iyyar ta ce tana ta ganin ana yada wannan batu, sai dai labarin babu gaskiya a ciki.

Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Ibrahim Abdullahi, shi ne ya musanta wannan labari a tattaunawarsa da BBC.

Kakakin ya ce: ''To abin da ke gaskiya shi ne ba rahoton gaskiya ba ne na cewa jam'iyyar PDP ta mika tiket dinta na takarar shugaban kasa zuwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ko tana kira da ya zo ya yi takarar a 2027 mai zuwa

BBC HAUSA 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org