Kaddara Ta Afkawa Jami’in Kwastam da matarsa da ‘ya’yansa huɗu suka rasu a gobara
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) reshen Jihohin Oyo/Osun, ta yi alhinin sanar da rasuwar jami’anta Kabiru Tijani, da matarsa, da ‘ya’yansu huɗu sakamakon wutar gobara da ta tashi.
A cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kayode Wey a ranar Talata 3 ga watan Disamba, 2024 a madadin shugaban hukumar kwastam na yankin, Kwanturola Ben Oramalugo, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin, 2 ga watan Disamba, 2024, da misalin karfe 3:00 na dare lokacin da gobara ta kama gidan su da ke Ede, jihar Osun.
Sanarwar ta ƙara da cewa, jami’in Kwatsam mai muƙamin SC, Kabiru Tijani, ya rike muƙamin jami’in kula da ayyuka na rundunar, inda ya ƙara da cewa, “SC Kabiru hafsa ne mai ƙwazo, jajircewarsa na gudanar da ayyukansa, musamman wajen hada kai da aiwatar da ayyukan yaki da fasakwauri da aka samu nasara, ya taimaka matuƙa, wajen samun nasarar ayyuka.”
“Matar sa, wacce ma’aikaciya ce mai himma a ƙungiyar matan jami’an kwastam (COWA) reshen Oyo/Osun, an yaba da irin gudunmawar da take bayarwa wajen kyautata rayuwar al’ummar rundunar Kwastam” cewar sanarwar.
A yayin da take bayyana wasu rahotannin da ake kyautata zaton na yadda gobarar ta afku, rundunar ta buƙaci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan rahotannin da ba su da tushe, domin abin da ya rage shi ne bayar da tallafi ga dangin waɗanda suka rasu da kuma ɗansa ɗaya tilo da ya tsira da ransa, kuma a ci gaba da bincike kan lamarin.
Kwanturola Ben Oramalugo, a madadin jami’ai rundunar da ɗaukacin ma’aikatan Kwatsam a Jihohin Oyo/Osun, ya jajantawa ‘yan uwa da abokanan marigayin.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa tuni aka yi jana’izar SC Kabiru Tijjani da iyalansa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
AiD Multimedia