Kafar Yanar Gizo Ta Facebook, Instagram da WhatsApp sun samu tangardar na’ura

 Miliyoyin masu amfani, manyan mahajojin kamfanin Meta da suka hada da Facebook da Instagram, da kuma WhatsApp, a fadin duniya na fuskantar tutsu.

Rahotannin da suka mamaye shafukan sada zumunta, ciki har da X, sun tabbatar da cewa lamarin ya zama kamar wutar daji, inda miliyoyin masu amfani suka kasa shiga shafukansu.

Wani dandali da ke bin diddigin abubuwan da suka faru, ya nuna yadda aka rinka tura rahotannin samun tangardar shafukan. 

Rahotanni sun nuna cewa masu amfani da Instagram sama da dubu 71 sun shigar da korafi game da tangardar,  yayin da masu amfani da Facebook suka aika korafe-korafe sama da dubu 107 daga sassan duniya.

DCL Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org