Kamfanonin sadarwa sun fara gargadin dakatar da ayyukansu a Najeriya sakamakon barazanar haraji da Gwamnatin Najeriya ta saka musu.
Ƙungiyar Masu Lasisin Ayyukan Sadarwa ta Najeriya (ALTON) ta yi gargaɗin cewa membobinta na iya fara "rage ayyuka"—wato dakatar da wasu ayyuka na sadarwa—idan ba a duba farashin sabis ba don daidaita shi da halin tattalin arziki na yanzu.
Shugaban ƙungiyar, Gbenga Adebayo, ya bayyana cewa masana’antar sadarwa tana fuskantar ƙara yawan kuɗaɗen gudanarwa, ciki har da hauhawar farashin makamashi, hauhawar farashin kaya, da kuma canjin kuɗi mai tsanani, duk da haka, farashin sabis bai canza ba. Ya jaddada cewa idan ba a sake duba farashin ba, masu ayyukan sadarwa za su iya rage ko dakatar da ayyuka a wasu yankuna da wasu lokuta, wanda hakan zai iya jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin rashin sadarwa. Wannan matsalar na iya shafar fannoni kamar tsaro, kasuwanci, lafiya, da ilimi, waɗanda ke dogaro sosai da kayan aikin sadarwa.
ALTON ta yi kira ga mahukunta da su gaggauta magance waɗannan matsalolin domin tabbatar da dorewar masana’antar sadarwa, wacce take da matuƙar muhimmanci ga ci gaban Najeriya. Ƙungiyar ta bayyana shirinta na yin aiki tare da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da makomar masana'antar.