Karon Farko Malam Nasiru El-Rufai yayi wankin babban bargo wa Tinubu.

 Bayan nuna son kai da Buhari yayi na fifita Yan arewa a mukaman Gwamnati a lokacinsa. 

Nasir el-Rufai ya soki Shugaba Bola Tinubu da girman kai da fifita mutanen kabilarsa ta Yarabawa a mukaman gwamnatin tarayya.

El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya bukataci  Tinubu ya daina amfani da siyasar bangaranci irin ta tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda ya fifita nadin 'yan arewa Musulmai a mukamai lokacin wa'adinsa. 


Malam Nasiru yayi wannan martani ne kan wani ra’ayi da fitacce marubuci a kafafen sada zumunta Farooq Kperogi yayi, wanda ke zaune a kasar Amurka dan asalin Najeriya.


El-Rufai ya zargi Tinubu da shirin nada wani dan Yarabawa a matsayin shugaban kamfanin NNPCL, el-Rufai ya rubuta a shafinsa na X wanda a baya akafi saninsa da( Twitter): El-Rufai ya ce “Gaba biyu ba sa gyara. Shigar da kowa cikin adalci ya fi kyau akan fifita wasu cikin girman kai.”


An zargi Tinubu da nada yan kabilar Yarabawa  a mafi yawancin mukamai.  Kamar yadda Buhar yayi a lokacinsa.


Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) da Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Najeriya (HURIWA) sun soki Tinubu kan fifita yankin kudu maso yamma a nadin mukamai, suna zarginsa da gudanar da siyasar bangaranci da rashin adalci.


Sai dai wasu masu suka sun zargi el-Rufai da cewa bai taba sukar Buhari ba a lokacin mulkinsa.


@ ATP Hausa

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org