Kasuwar Kirifto (crypto) ta Bude Inda Shugaba Donald Trump Ya Sha Alawashin Bunkasa Harkokin Crypto

 Muna Taya masu rike  Bitcoin da sauran kasuwar Kirifto murna in ji Trump bayan da farashin bitcoin ya tsallake sama da $100,000

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump a ranar Alhamis din nan ya jinginawa masu rike da Bitcoin tare da Taya murna bayan da bitcoin din ya Kafa Tarihi ya wuce dala 100,000, yana bayyana wa mabiyan sa na dandalin sada zumuntar X Yana Mai cewa "barka da ku" bayan da cryptocurrency ya tsallake sama da kashi 50 tun bayan nasarar zabensa.

Bitcoin ya Kafa Tarihi ne a karon farko inda ya tsallake farashin $100,000 a karon farko ranar alhamis bayan Trump ya zabi Paul Atkins mai goyon bayan cryptocurrency don shugabantar kula da harkokin tsaro na Amurka, wanda ke karfafa kyakkyawan fata shugaban mai jiran gado bunkasa fannin.

Ƙungiyar dijital ta ji daɗin Kalaman na sa tun bayan zaben Nuwamba 5 na Trump, wanda ya yi alkawarin sanya Amurka ta zama wata alkaryar "bitcoin da cryptocurrency a duniya".

Bitcoin ya buga dala 103,800.45 a cikin sa'o'in kasuwancin Siya da Siyarwa ranar Alhamis kafin ya koma kusan dala 101,000.

Bayan kalaman na Trump, ya sake hawa, inda ya kai dala 103,320.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org