Kofa Ya Nemi Gafara Bisa Zakewarsa Kan Kudirin Harajin Na Tinubu
Dan majalisar wakilai mai wakiltar jihar Kano Abdulmumin Jibrin Kofa ya nemi gafarar jama'a dangane da maganganun da ya yi ta yi na goyan bayan sabon kudirin haraji da shugaban Tinubu ya bijiro.
Jibrin Kofa na sawun gaba wajen zaƙewa ga goyan bayan ƙudirin, ya ce ba wai yana goyan bayan dukkanin dokar haraji bane, sai dai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga Arewa da Najeriya.
Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce duk da haka, yana bai wa duk waɗanda matsayarsa a kan dokar ta ɓata wa rai,hakuri.
Kofa ya kuma yaba wa shehin Malamin nan Alƙali Salihu Abubakar Zariya bisa jajircewa wajen faɗakarwa.
Ya ƙara da gode wa Jagoran jamiyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso saboda shawarar da ya basa a kan batun.