Kotu a Legas ta yanke wa ma'aurata hukuncin ɗaurin shekaru 16 sakamakon damfarar Naira Miliyan 52

 Kotun Musamman ta Laifuka da ke Ikeja, Jihar Legas, ta yanke wa wasu ma'aurata, Harry Uyanwanne da Oluwakemi Odemuyiwa (wanda aka fi sani da Kristein Uyanwanne), hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 16 a hade saboda satar Naira miliyan 52.

Mai shari’a Mojisola Dada ta yanke wa su biyun hukunci tare da wani coci mai suna Temple International Church.

Haka kuma, Mai shari’a Dada ta bayar da umarni cewa a soke rajistar cocin na uku kuma a rufe shi gaba ɗaya saboda amfani da sunan Allah da coci wajen damfarar mutane.

Lokacin da ta ke bayar da hukunci, Mai shari’a ta samu waɗanda ake tuhuma ukun da laifi bisa tuhume-tuhume bakwai da hukumar EFCC ta gabatar a kansu.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da ma'auratan a ranar 25 ga Fabrairu, 2020. A yayin gurfanar da su, sun musanta zargin da ake musu, wanda ya sa aka fara shari'a.

A lokacin shari’ar, lauyan EFCC, Babatunde Sonoiki, ya gabatar da shaidu biyar yayin da lauyan masu kare kansu ya gabatar da shaidu biyu.

Mai shari’a ta bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin da ake tuhuma cikin gamsasshen shaidu, don haka ta same su biyu da laifi.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org