Kungiyar kare Haƙƙin bil'adama ta NHRC tayi Allah wadai da zargin da ake jinginawa Lauya Falana da farfesa Wole Soyinka.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi ta hannun Taiwo Adeleke da Digifa Werenipre, shugabannin kungiyar NHRC, kungiyar ta nuna damuwa kan “zargin da ake yawan yi” cewa Soyinka da Falana sun yi shiru a lokacin da Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki.
NHRC ta ce Soyinka da Falana tun shekaru aru-aru suna kan gaba wajen gwagwarmayar neman shugabanci nagari.
Kungiyar ta bukaci matasa su koyi darasi daga Omoyele Sowore, wanda ya kafa kungiyar #RevolutionNow, ta hanyar yaki da son kai don tabbatar da adalci da daidaito.
“Za mu so mu tunatar da wadannan mutane, musamman matasa, cewa ayyukansu na kasancewa koma baya ga tarihi mai daraja na gwagwarmayar dimokradiyya da wadannan shugabanni biyu suka wakilci tarihin Najeriya,” kamar yadda sanarwar ta ce.
“Muna kira ga matasa suyi koyi daga Mr. Omoyele Sowore da su kwaikwayi gudummawarsa mai kyau ga dimokradiyya da adalci tsawon shekaru sama da talatin.”
NHRC ta ce lokaci ya yi da Soyinka zai huta, yayin da Falana ya ci gaba da fafutuka ta hanyar ɗaukar shari’o’i kyauta, har ma da wasu da suka saba wa gwamnatin yanzu.
Kungiyar ta kalubalanci masu suka da su zama masu kwazo da jagorantar zanga-zangar da suke so, maimakon su dinga sukar “mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu sau da dama” don ƙasar ta inganta.