Kungiyar Mahukuntar nukiliya ta duniya ta ce take-taken Iran abin damuwa ne

Jagoran hukumar kula da nukiliya ta duniya, IAEA, ya sheda wa BBC cewa shawarar da Iran ta yanke ta aikin samar da ingantaccen sinadarin uranium babban abin damuwa ne sosai.

Rafael Grossi, ya ce Iran na kara tara sinadarin da ta inganta shi zuwa kashi 60 cikin dari, wato matakin da ya rage dan kadan ya kai wanda ake samar da makaman nukiliya da shi.

Da dama a wannan yanki za su kalli abin da Iran din ke yi a matsayin wani martini na koma-bayan da ta samu a bangaren soji da diflomasiyya a Syria da Lebanon da Gaza a 'yan watannin nan.

Mista Grossi ya ce wannan ba wani boyayyen abu ba ne cewa wasu 'yan siyasa a Iran na neman kasar ta kera makamin nukiliya – to amma bayan tattanawa a Tehran a makon nan, shugaban na hukumar nukiliya ya ce to amma bisa ga dukkana alamu wannan ba kuduri ba ne ko aniya ta shugabancin kasar na yanzu.

Mr Grossi na Magana ne a gefen taron tattaunawar Manama a Bahrain, taron da Cibiyar Nazarin Dabaru ta Duniya da ke London ( International Institute for Strategic Studies)

Ya gargadi Isra'ila da ta guji kai wa cibiyoyin nukiliya na Iran hari, yana mai cewa abin da zai iya biyo baya zai zama mai tayar da hankali sosai, ta ramuwar gayya da kuma bazuwar tururin nukiliyar.

Haka kuma ya ce yanzu abu ne yanzu da ya zaman a damuwa ainun, ganin yadda karin kasasahe na tunanin mallakar makaman nak are-dangi – inda yanzu maganar mallakar ma ta zama abar yi a fili ta ma zama tamkar al'ada.

A wani rahoto da ya bai wa manyan shugabannin hukumar ta nukiliya ta duniya, Mista Grosii ya ce jami'ansa masu Sanya -ido sun tabbatar masa da cewa Iran na kara aikin hada sinadarin na uranium a cibiyarta ta nukiliya ta Fordow da ke kudu da Tehran.

@BBC HAUSA 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org