Legas ta cancanci gwamna Musulmi a 2027 - Babban Limamin Coci
Wani babban limamin cocin ta ƙasa da ke Legas, Acibishof Isaac Ayo Olawuyi, ya yi kira ga a zaɓi musulmi a matsayin gwamnan jihar musulmi zaben 2027.
A cewar Olawuyi , idan 2027 ta zo, ya zama shekaru 12 kenan da Kiristoci ke mulkar Legas.
Limamin ya bayyana haka ne a yayin taron addu'a da godiya na shekara karo na 22 na majalisar dokokin Legas mai taken: ‘Muryar Rahama’.
Babban sakataren yada labarai na kakakin majalisar, Mudashiru Obasa, Eromosele Ebhomele ne ya bayyana hakan ga wakilin Daily Trust a yau Asabar.
Olawuyi ya ba da shawarar cewa zabar Musulmi a matsayin gwamna a 2027 zai wanzar da zaman lafiya da kaunar juna tsakanin addinai.