Magance matsalar makamashi ne zai inganta tattalin arzikin Najeriya – Shettima
Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ya ce Najeriya ba za ta samu cigaban tattalin arzikin da ake buƙata ba sai an inganta ɓangaren makamashinta.
Sai ya yi kira ga shugabanni a ƙasar da su ajiye bambancin siyasa, domin yaƙi da matsalar da ɓangaren makamashin ke fuskanta.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin majalisar tattalin arzikin Najeriya kan wutar lantarki da na yaƙi da polio a fadar shugaban ƙasar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
“Lallai ba za a iya inganta tattalin arzikin ƙasar nan ba sai mun magance matsalar makashi, sannan mu tabbatar dukkan ƴan Najeriya suna samun isasshen makamashin da suke fuskanta," in ji shi.
Da yake bayyana takaicinsa kan yadda kashi 40 zuwa 70 na ƴan ƙasar suke fama da ƙarancin wutar lantarki, Shettima ya ce ganin gwamnoni da sauran waɗanda suke cikin kwamitin ya sa ya samu natsuwar za a magance matsalar.