Majalisar Dattawa ta yanke shawarar tattaunawa da Ministan Shari'a don yin gyare-gyare akan kudirorin dokar haraji

Majalisar Dattawa ta yanke shawarar ganawa da Antoni janar na kasa a ranar Alhamis mai zuwa domin warware sabanin da ke akwai game da dokar gyaran haraji da aka gabatar.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, yayin jagorantar zaman majalisar a ranar Laraba, ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan jerin taruka da majalisar ta gudanar kan gyaran haraji da aka gabatar.

Har ila yau, ya sanar da kafa wani kwamiti kan wannan batu, wanda Sanata Abba Moro, Shugaban ‘Yan Adawa a Majalisar Dattawa, zai jagoranta.

A halin da ake ciki, an umarci Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa da ya dakatar da duk wani aiki na dokoki kan gyaran harajin har sai bayan sakamakon taron da Antoni Janar ya fito fili.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org