Majalisar Wakilai ta buƙaci CBN ya dakatar da yi wa ma’aikata 1,000 ritaya

 Majalisar wakilai ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dakatar da shirin ritayar ma’aikata 1,000.

A cewar rahotanni, babban bankin ya shirya tsaf don ritayar ma’aikatan tare da samar musu da kudin fansho da ya kai sama da naira biliyan 50.

A zaman majalisar da aka yi ranar Talata, majalisar ta yanke shawarar kafa kwamitin wucin gadi domin binciken tsari da halaccin wannan aikin, tare da tabbatar da gaskiya, adalci, da kuma yin amfani da kudade yadda ya kamata.

Majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan amincewa da kudurin gaggawa da Kama Nkemkama daga Jihar Ebonyi ya gabatar.

An amince da kudurin ne ta hanyar kada kuri’ar baki da Tajudeen Abbas, kakakin majalisar, ya jagoranta.

Saboda haka, majalisar ta bukaci ma’aikatar kwadago da ayyuka da ta kare hakkokin ma’aikatan da abin ya shafa.

Kwamitin da za a kafa yana da makonni hudu don gudanar da bincike tare da gabatar da rahoto ga majalisar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org