Maryam Kurfi : Ƴar Jihar Katsina Ta Da Farko Ta Shiga Takarar Gasar Sarauniyar Kyau Ta Najeriya

Maryam Sulaiman Kurfi wacce ƴar asalin ƙaramar hukumar Dutsinma ce a Jihar Katsina, ta kasance mace ta farko ƴar asalin Jihar Katsina da ta shiga gasar sarauniyar kyau ta (45) a Najeriya wadda kuma tuni ta tsallake matakin farko da na biyu na tantancewa, yanzu haka tana cikin mataki na ƙarshe a sansanin tantancewa da ke Jihar Legas wanda daga nan ne kuma za a bayyana sakamakon gasar.

An dai haifi Maryam a garin Abuja ta kuma samu nasarar kammala karatunta na digirin farko kan ilimin jagoranci da daidaita tunanin al’umma, ma’ana (Guidance and counselling) a Jami’ar Jihar Nasarawa. Yanzu haka tana da kimanin shekaru 20 a Duniya.

A rahotannin da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, ana kyautata zaton Maryam ɗin za ta samu nasarar lashe gasar wanda in hakan ta tabbata za ta zama sarauniyar kyau ta farko a Najeriya daga Jihar Katsina.

DAGA Shafin Dokin Karfe TV

Wane fata zaku yi mata?

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org