Matar Shugaban Kungiyar Fulani Ta Yi Ikirarin Cewa "Mijina ba ɗan Ta'adda ba ne"
Iyalan Shugaban kungiyar Fulani ta miyatti Allah Kautel Hore ta kasa, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo sun nemi Jami'an Sojin Najeriya akan su saki Bodejon.
Uwar gidan Shugaban Fulanin Hajiya Hauwa Bodejo ta bayyana cewa mijinta ba ɗan ta'adda bane mutum ne amintacce kamar sauran yan kasa Nagari.
Uwargidan Bodejo ta bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu, Yan majalisun Najeriya su shiga tsakani don kawo karshen cin zarafin mijinta akan laifin da bai aikata ba.
Ta roki a sake shi ba tare da wata sharadi ba, daga karshe ta bayyana halin matsanancin rashin lafiya da mijinta ke fama da shi tun kama shi na farko har izuwa yanzu yana karbar magani.
Ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ta kira a babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis. 11 ga watan Disamba 2024.
ATP Hausa Flash News.Ng