Matsalar tattalin arziki: Tinubu ya fara gano bakin zaren - Abdulsamad BUA

 Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabi'u ya baiyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya fara gano bakin zaren matsalar tattalin arziki a Nijeriya.

PREMIUM TIMES ta rawaito cewa shugaban na BUA ya baiyana hakan ne lokacin da ziyarci Tinubu a gidansa da ke Legas a juya Juma'a, inda ya ce gyaran tattalin arziki da Tinubun ke yi akwai raɗaɗi, amma kuma ha zama dole.


A cewar Abdulsamad, "Duk da dai mun san cewa wasu gyare-gyaren da mai girma shugaban ƙasa ke yi na da raɗaɗi, amma wadannan gyare-gyaren, a bangarenmu mu ƴan kasuwa ya zama wajibi.


"Gaskiya ne cewa wasu daga cikinsu suna da zafi sosai, amma muna bukatar wadannan sauye-sauye, musamman haɗe kasuwar musayar kudaden waje."


“Za ku tuna cewa farashin canji da, a kan N500 ne a babban bankin kasa, amma a waje ya kai N800. Hakan bai dace ba. Don haka a zahiri an hade hakan kuma da farko abu ne mai wahala, tunda sai da muka ga farashin canji ya kai ga kusan Naira 2000, yanzu an tsayar da ma’auni, yanzu dala daya kusan N1,500 ce zuwa N1,550 kuma na tabbata za mu ci gaba da ganin farashin na sauka, har ma ƙasa da haka."


“Don haka na yi imanin cewa wasu daga cikin wadannan sauye-sauyen… a, da farko dai gaskiya da wuya,  amma abubuwa sun fara sauki a yanzu, kuma ina da kwarin gwiwa cewa abubuwa za su yi kyau a Najeriya. 

"Shugaban kasa yana yin abubuwa da yawa, hakika gwamnati na yin kokari matuka wajen ganin an samu gyara da daidaito cikin tattalin arziki da sauran bangarorin tattalin arziki,” in ji shi.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org